Cikin sanarwar, kwamitin sulhun ya nuna yabo kan babbar gudummawar da rundunonin sojoji na wasu kasashen duniya suka bayar wajen yaki da kungiyar Boko Haram yadda ya kamata, ya kuma bukaci kungiyoyin shiyya-shiyya da abin ya shafa da su ci gaba da yin hadin gwiwa kan yakin da ake da kungiyar. A sa'i daya kuma, kwamitin ya bukaci gamayyar kasa da kasa da masu samar da taimakon kudade da su goyi bayan rundunonin sojojin, kana su samar da kudade a yayin taron samar da tallafin kudi da kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU za ta kira.
Bugu da kari, kwamitin ya sanar da cewa, kungiyar Boko Haram ta haddasa mummunar illa ga harkokin jin kai a wasu kasashen dake yankin tafkin Chadi, inda kimanin mutane miliyan 1.9 suka bar gidajensu, dangane da haka, kwamitin sulhu ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su taimaka wa rundunonin sojojin da ke aikin kiyaye tsaro a yankin, da kuma tabbatar da isar da taimakon jin kai, ta yadda 'yan gudun hijira za su iya komawa gidajensu ba tare da wata matsala ba. (Maryam)