in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani harin ta'addanci ya halaka mutane 8 a arewacin Najeriya
2015-07-25 13:01:51 cri
A kalla mutane takwas da suka hada da wani mai garin wurin suka mutu a cikin wani harin da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram da kai wa a wani kauyen jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, a cewar wata majiyar tsaro a ranar Jumma'a.

Mayakan da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram sun kai wani samame a Pompomari mai tazarar kilomita kimanin 12 daga birnin Biu kana kuma kilomita kimanin 187 daga kudancin babban birnin Jihar, wato Maiduguri, in ji wannan majiya.

Danladi Ali, wani mazaunin Biu, ya bayyana cewa kawunsa na daga cikin wadanda suka mutu. Sun kashe mutane da dama, da suka hada da mahaifiyinsa da babban wansa. A dunkule, mutane tara, har da mai garin kauyen aka kashe, in ji Danladi Ali.

Kungiyar Boko na ci gaba da zafafa hare harenta a Borno, birnin asalin shugaban rundunar sojojin da aka nada bada jimawa ba ya fito, janar Tukur Buratai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China