A ranar Jumma'a ce ofishin kare 'yancin bil-adama na MDD ya nuna damuwa dangane da yawan mutane da suka mutu ciki har da fararen hula da kuma lalata gidaje da kadarori masu dimbin yawa gami da rashin muhalli da suka auku a kasar Najeriya a cikin 'yan makonnin nan.
Mai Magana da yawun MDD Martin Nesirky yayin jawabi ga 'yan jarida da aka saba yi kullum ya ce, ofishin kare 'yancin bil-adama na kira ga gwamnatin Najeriya da ta tabbatar cewa kokari da take yi a fuskar tabbatar da tsaro basu saba ka'idojin kare 'yancin bil-adama ba.
Mutane 185 ne suka mutu, ga gidaje dubu 2 da aka kona da kuma Babura 486 da aka lalata yayin wata arangama tsakanin jami'an sojin kasar Najeriya da 'yan tawaye, wanda ya auku a daren 16 ga watan Afrilu aka kuma ci gaba da hakan na wasu karin kwanaki a garin Baga dake kan iyaka a arewa maso gabashin Najeirya.
Ofishin kare 'yancin bil adaman ya ci gaba da cewa, wannan rikici ya taso ne bayan da 'yan kungiyar Boko Haram suka kasha wani soja yayin sintiri.Wannan fada na daga cikin mafi kazanta tun lokacin da kungiyar ta kaddamar da tada kayar baya a shekarar 2009.
Ofishin na MDD ya bukaci jami'an tsaro da sojoji da su kiyaye 'yancin bil-adama su kuma daina amfani da karfin soja fiye da kima a irin wannan aiki, domin irin wannan sintiri na ruruta wutar gaba, musamman ma idan aka kashe farar hula ko aka lalata kadarorinsu, inji Nesirky.
Da kuma yake yaba mataki da gwamnati ta dauka na kafa kwamitin fara tattaunawa da kungiyar Boko Haram, ofishin kare 'yancin bil-adama ya kuma bukaci hukumomin Najeriya da su tabbatar da cewa an hukunta masu take 'yancin bil-adama.(Lami Ali)