in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Akalla mutane 29 ne aka hallaka a yayin wasu sabbin hare-hare
2015-07-28 20:59:47 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa mutane akalla 29 ne suka rasa rayukan su, kana wasu da dama suka samu raunuka, sakamakon wasu hare-haren da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne suka kaddamar da su, a wasu kauyukan dake kewayen karamar hukumar Askira Uba a jihar Borno.

Wasu shugabannin yankin sun tabbatarwa majiyar mu aukuwar hare-haren na jiya Litinin da kuma safiyar Talatar nan. Wakilin yankin a majalissar dokokin Najeriya Jubrin Satumari, ya shaidawa kamfanin dillancin labaru na Sin cewa, maharan sun aukawa kauyen Dille da wasu kauyuka da dama, inda suka rika latata dukiyoyi da gine-ginen al'umma.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China