in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban rundanar sojojin kasar Najeriya ya lashi takobin yaki da masu taka kayar baya
2015-07-19 17:54:29 cri
Rundunar sojojin Najeriya na da niyyar sake duba dabarunta na gudanar da ayyukanta domin kare kowa ne yanki na fadin kasar Najeriya dake fuskantar barazanar masu ta da kayar baya, in ji janar Tukur Buratai da aka nada shi sabon shugaban rundunar sojijin Najeriya ba da jimawa ba. Janar Buratai ya bayyana ra'ayinsa a ranar Jumma'a a birnin Damaturu, hedkwatar jihar Yobe da ke arewa maso gabshin Najeriya, inda aka kai wasu tagwayen harin kunar bakin wake da ya halaka musulmi da dama.

Sabon shugaban rundunar sojojin Najeriya, ya bayyana niyyarsa na kafa wata sabuwar rundunar sojoji mai cike da kwarewa da za ta tashi tsaye wajen daukar nauyinta kamar yadda dokokin kasa suka tanada, bisa babbar akidar bautawa kasa yadda ya kamata. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China