Bayan wani hari da kungiyar kishin islaman ta kai a ranar Laraban da ta gabata a garin Gamgara na jihar Bosso mai iyaka da Najeriya, wanda cikinsa aka yi wasu mazauna kauye goma yankan rago, jami'an tsaro na FDS sun gudanar da wasu ayyukan kakkabe masu tada kayar baya daga ranar 15 zuwa 17 ga watan Yulin da ya gabata, a kan tsawon tafkin Komadougou Yobe, da ke kan iyaka tsakanin Nijar da Najeriya. A cewar sanarwar da aka fitar a ranar Asabar a gidan rediyo da talabijin na kasar Nijar (ORTN), adadin wucin gadi na mayakan Boko Haram da aka kashe ya kai 32, tare da cafke wasu mutane uku da suka hada da wani shugaban kungiyar, da babura 27, da kuma lalata tarin kayayyakin yaki na wannan kungiyar. (Maman Ada)