in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Girka
2014-07-14 10:57:19 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Girka Karolos Papoulias a tsibirin Rhode dake kasar Girka, inda shugabannin biyu suka yi shawarwari, tare da musayar ra'ayoyi da cimma daidaito kan raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da manyan batutuwan duniya, da kuma na shiyya-shiyya masu muhimmanci gare su.

Yayin ganawar shuwagabannin biyu a jiya Lahadi, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, Sin da Girka kasashe ne biyu dake rike da al'adun gargajiya, wadanda kuma suka kirkiro al'adun musamman da suka yi babban tasiri ga al'adun bil Adama. Ya ce, jama'ar kasashen biyu suna kauna da girmama juna, kuma wannan dangantakar abokantaka dake tsakaninsu na fadada yadda ya kamata.

A nasa bangare, shugaba Papoulias ya bayyana cewa, jama'ar kasarsa ta Girka, na jinjinawa al'adun gargajiya na kasar Sin, da nasarorin da Sin ta samu wajen ginuwa a zamanance, tare da muhimmancin rawar da take takawa a harkokin duniya.

Kaza lika shugabannin kasashen biyu sun bayyana cewa, za su ci gaba da yin kokari wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashensu, da ma kasashen Turai baki daya. Bugu da kari sun bayyana kudurin samar da zaman lafiya, a matsayin buri da kasashen ke fatan jama'ar kasashen duniya za su cimma. Kana sun bayyana bukatar watsi da yunkurin goyon bayan yakin fascist, tare da rungumar tabbatar da zaman lafiya a fadin duniya baki daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China