A wannan gaba ana kara fahimtar ra'ayin bangarori daban daban game da kasar ta Girka, inda da dama ke fatan Girkan za ta iya kaddamar da wani cikakken shirin kwaskwarima wanda zai dace, domin ci gaba da zama a yankin dake amfani da kudin Euro.
Game da hakan, shugabar asusun IMF Christine Lagarde, ta bayyana cewa asusun ba zai baiwa Girka gatanci na musamman ba, don haka dole ne kasar ta sauya tsarin biyan bashin ta, kafin a tsai da niyyar ci gaba da baiwa kasar bashin da take bukata. Shugabar ta kuma kara da cewa, ko da yake kasar Girka ta saba yarjejeniyar bashin dake tsakaninta da IMF, kuma ta ki amincewa ta aiwatar da shirin samun kudade ta hanyar kwaskwarima bayan jefa kuri'ar raba gardama, a daya bangaren asusun na IMF zai ci gaba da taimakon ta wajen zakulo wani shiri da ya dace, wanda kuma zai iya tabbatar da zaman karko, da sake farfadowar tattalin arzikin ta, tare kuma da neman dauwamammen ci gaba a harkar bashin na ta.
A nasa bagare, firaministan kasar Girka Alexis Tsipras, ya sake nanatawa a gaban majalissun dokokin Turai cewa, kasarsa ba ta son fitowa daga tarayyar kasashe masu amfani da kudin EURO.
Manazarta na ganin cewa, idan har kasar Girka na son ci gaba da zama a yankin dake amfani da kudin na EURO, to ya zame mata dole ta biya bukatun masu bin ta bashi, musamman a fannin kaddamar da wani shiri wanda zai dace, ta kuma karfafa musu kwarin gwiwa bisa kan ta. (Bilkisu)