Shugabar asusun bada lamuni na duniya wato IMF Christine Lagarde ta bayar da sanarwa a jiya Lahadi cewa, ta aikawa kwamitin gudanarwar asusun sako game da kasa samun wani sakamako a shawarwarin da ake na taimakawa kasar Girka, kana ta nuna bakin ciki game da batun, amma ta yi alkawarin ci gaba da tuntubar gwamnatin kasar Girka.
Madam Lagarde ta yi maraba da sanarwar da kungiyar kasashe masu amfani da kudin Euro da babban bankin nahiyar Turai suka bayar na tabbatar da yanayin karko a yankin da ake amfani da kudin Euro ta hanyar daukar dukkan matakan da suka dace. Kana IMF za ta ci gaba da sa –ido kan halin da ake ciki a kasar Girka da sauran kasashen da abin ya shafa, da kuma shirya samar da tallafin da ake bukata.
Hakazalika kuma Lagarde ta jaddada cewa, IMF yana shirya ci gaba da yin shawarwari tare da gwamnatin kasar Girka da bangarori daban daban na nahiyar Turai kan wannan batu, amma ta ce ana bukatar kasar Girka da ta yi kwaskwarima kan tsari da harkokin ta na kudi.
Firaministan kasar Girka Alexis Tsipras ya yi jawabi ta telebijin a daren ranar Lahadi cewa, bankunan kasar Girka za su dakatar da ayyukansu da daukar matakin sarrafa kudi bisa shawarar da babban bankin kasar ya gabatar. (Zainab)