in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya bayyana ra'ayin gwamnatinsa kan matsalar yawan cin bashi a Girka
2015-06-30 10:42:11 cri

A yammacin ranar Litinin bisa agogon Turai, firaministan kasar Sin mista Li Keqiang ya yi bayani kan ra'ayin gwamnatinsa dangane da matsalar yawan cin bashi a kasar Girka.

Firaministan ya ce, kasar Sin a matsayinta na babbar kawar hadaddiyar kungiyar kasashen Turai EU a fannin manyan tsare-tsare da cinikayya, a ko da yaushe tana goyon bayan kasashen Turai kan kokarinsu na dunkulewa a waje guda, kuma tana son ganin wata nahiyar Turai mai walwala, da kungiyar EU da mambobinta ke zaman tsintsiya madaurinki daya, gami da kudin Turai Euro mai karfi.

Haka zalika, Li ya jaddada cewa, kasar Sin na fatan ganin Girka ta tsaya cikin yankin kudin Euro, kuma ta yi kira ga bangarorin da suka ba da basusuka da kasar Girka ita kanta don su yi kokarin cimma matsaya cikin sauri, ta yadda za a samu damar taimakawa kasar da yankin kudin Euro baki daya fitowa daga mawuyacin hali. Dangane da hakan, firaministan kasar ta Sin ya ce, kasarsa na son taka rawar a-zo-a-gani.

Firaminista Li Keqiang ya yi zancen ne bayan da ya gana da shugaban majalisar nahiyar Turai Donald Tusk da shugaban kwamitin kungiyar EU Jean- Claude Juncker a birnin Brussels na kasar Belgium. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China