Tun karfe bakwai da safe har zuwa karfe 7 da dare a yau, za'a ci gaba da gudanar da zaben a kasar ta Girka, kuma bisa kididdigar da hukuma mai kula da harkokin cikin gida ta kasar Girka ta yi, an ce, adadin jama'ar kasa dake da ikon kada kuri'u ya kai kimanin miliyan 9 da dubu 800, haka kuma shirya zaben cikin gajeren lokaci, ya sa, 'yan kasar Girka dake ketare ba za su samu damar kada kuri'u kan zaben raba gardamar ba.
Bisa dokokin kasar, sai a kalla adadin masu kada kuri'u ya kai kashi 40 bisa dari, sannan sakamakon zaben zai yi tasiri ga makomar kasar.
Haka kuma, bisa binciken da aka yi dangane da jin ra'ayin jama'ar kasar Girka, an ce, adadin masu amincewa da na masu rashin amincewa na kunnen doki, shi ya sa, ba za a iya yin wani hasashe kan sakamakon zaben din ba. (Maryam)