Fadar firaministan kasar Girka ta bayar da samarwa cewa, gwamnatin Girka ta bada shawarar cimma yarjejeniya ta shekara 2 tare da tsarin tabbatar da hada-hadar kudi na Turai wato ESM don ganin ba ta saba yarjejeniya har ma ta fita daga cikin rukunin kasashe masu amfani da kudin Euro ba.
Sanarwar ta kara da cewa, gwamnatin kasar Girka za ta yi kokarin laubo hanyoyin warware matsalar, kuma kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a game da daftarin yarjejeniya ba shi ne karshen shawarwarin game da matsalarta ba.
Shugaban kungiyar kasashe masu amfani da kudin Euro Jeroen Dijsselbloem ya bayyana a wannan rana cewa, kungiyarsa za ta kara tattaunawa da mambobinta ta wayar tarho a yau Laraba don duba sabuwar shawarar da kasar Girka ta gabatar game da yadda za a taimaka mata. Ya bayyana cewa, tilas ne a bukaci karin sharadi masu tsanani wajen cimma sabuwar yarjejeniyar taimakawa kasar Girka, kuma ya kamata gwamnatin kasar Girka ta canja matsayinta a siyasance. (Zainab)