Bisa sakamakon zaben raba gardama, wanda ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Girka ta fitar da safiyar Litinin din nan, an ce sakamakon zaben ya nuna kin amincewar 'yan kasar game da daftarin yarjejeniyar samun kudin biyan bashin kasar ta hanyar yin kwaskwarima.
Yayin kuri'ar ta raba gardama da aka kada a jiya Lahadi 5 ga wata, masu nuna rashin amincewa sun yi rinjaye. Bisa kididdigar da aka yi kan kashi 94 bisa dari na dukkan kuri'un da aka jefa, kuri'un kashi 61.3 cikin dari sun nuna rashin amincewa ga daftarin, yayin da kashi 38.7 cikin dari suka goyi bayan hakan. Har wa yau kashi 62.5 cikin dari na dukkan jama'ar kasar sun jefa kuri'un su a zaben.
Firaministan kasar Girka Alexis Tsipras ya yi jawabi ta telebijin bayan kammala fidda sakamakon zaben, inda ya ce jama'ar kasar Girka sun nuna rashin amincewa ga ka'idojin biyan bashin, koda yake baya nufin sanya Girka ta ware daga nahiyar Turai, sai dai kawai hakan na nufin kasar na burin ganin bangarorin biyu sun cimma yarjejeniya da ta dace.
Ya kara da cewa, wannan sakamako na zabe zai karfafa matsayin gwamnatin kasar Girka wajen gudanar da shawarwari a wannan fanni, da cimma yarjejeniyar bashi tare da masu samar da bashin cikin hanzari.
A daya hannun kuma, ministan kudin kasar Girka Yanis Varoufakis, ya bayyana cewa kasar sa ta shirya cimma yarjejeniyar da za ta samar da moriya ga kan ta, da kuma masu bata bashi.
Bugu da kari kwamitin kungiyar EU ya fidda wata sanarwa, wadda ke cewa kwamitin na girmama sakamakon zaben raba gardama da aka gudanar a kasar Girka. Kana sanarwar ta ce shugaban kwamitin Jean-Claude Juncker, zai tattauna tare da shugabannin sauran kasashe 18 na yanki mai amfani da kudin Euro, da shugabannin hukumomin kungiyar EU a daren Litinin din nan game da batun matakin da Girkan ta dauka. (Zainab)