in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin harkokin waje na Sin da Botswana sun gana da juna
2015-06-20 14:05:08 cri
Ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya gana da takwararsa ta kasar Botswana Pelonomi Venson-Moitoi wadda ke ziyarar aiki a nan birnin Beijing.

Yayin ganawar tasu, Mr Wang ya ce, bunkasuwar Sin na ba da gudunmawa sosai ga bunkasuwar kasashe masu tasowa da kiyaye zaman lafiyar duniya, kuma hakan na ba da taimako ga bunkasuwar aminanta a nahiyar Afrika.

Bugu da kari ya ce Sin na yin iyakacin kokarin gudanar da hadin gwiwar samun moriyar juna tsakaninta da kasashen Afrika, domin kyautata halin da kasashe masu tasowa suka dade suka fuskanta na rashin samun adalci, har ma da sa kaimi ga kafa wani tsari a duniya mai adalci da daidaito.

A nata bangare Madam Venson-Moitoi ta bayyana godiya sosai bisa ga taimakon da Sin ke baiwa kasarta na dogon lokaci, kuma ta yabawa gudunmawa da Sin ta bayar ta fuskar raya Afrika karkashin tsarin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika.

Ministar harkokkin wajen kasar ta Kasar Botswana ta kuma bayyana fatan kara hadin gwiwa da kasar Sin domin kara amincewa da juna a siyasance, da zurfafa fahimtar juna, sannan kuma da habaka hadin gwiwa a fannoni daban-daban har ma da sa kaimi ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China