in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta tura ma'aikatan kiwon lafiya karo na 14 Botswana
2015-02-15 10:17:15 cri

Gwamnatocin kasashen Sin da Botswana sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar tura tawagar ma'aikatan kiwon lafiya karo na 14 zuwa kasar Botswana.

Jakadan kasar Sin da ke Botswana Zheng Zhuqiang da ministar kiwon lafiya ta kasar Botswana Dorcas Makgato-Malesu ne suka sanya hannun a Gaborone, fadar gwamnatin kasar a madadin kasashensu.

A jawabinta, Makgato-Malesu ta godewa gwamnatin kasar Sin da wannan tallafi, wanda ta ce, ya taimaka wajen bunkasa harkokin kiwon lafiyan kasar tun lokacin da kasar Sin ta fara turo tawagar lafiya kasar a shekarar 1981.

Shi ma a nasa jawabin, jakadan Sin a kasar ta Botswana Zheng Zhuqiang ya ce, bangaren lafiya na daga cikin sassa masu muhimmanci da Sin ke taimakawa Botswana, kuma kasar ta Sin na duba yiwuwar tura kwararrun ma'aikatan lafiya na gajeren lokacin kasar ta Botswana.

Ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki da Botswana wajen kara karfafa hadin gwiwa a fannoni daban-daban, ciki har da bangaren kiwon lafiya.

Rukuni na 14 na ma'aikatan kiwon lafiyan da Sin za ta tura kasar ta Botsawana dai na kunshe ne da likitoci 30, nas-nas 10 da ma'aikata 6. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China