Ma'aikatar lafiya ta kasar Botswana ta yaba da irin gudumawar da tawagar ma'aikatan lafiya ta kasar Sin da ke aiki a kasar suka bayar.
Ministar lafiyar kasar Botswana Dorcas Makgato ce ta bayyana hakan yayin wata liyafar ban-kwana da aka shiryawa rukuni na 13 na tawagar ma'aikatan lafiyar kasar Sin da ke Botswana, don nuna godiya kan irin gudummawar da suka ba da a lokacin da suke aiki a asibitin ginbiya Marina da ke Gaborone da kuma asibitin Nyangabgwe a Francistown, birni na biyu mafi girma a kasar ta Botswana.
Madam Dorcas ta ce, a shekarar 1985 ne rukuni na farko na ma'aikatan lafiyar kasar Sin ya fara aiki a kasar Botswana da ma'aikata 13, inda adadin ya karu zuwa 46, lamarin da ke nuna ingantuwar dangantaka tsakanin Sin da kasar Botswana.
Shi ma da yake jawabi, jakadan Sin a kasar Botswana Zheng Zhuqiang ya ce, bangaren kula da lafiyar al'umma, shi ne muhimmin sashin hadin gwiwa tsakanin sassan biyu.
A karshen liyafar, ministar lafiyar kasar Botswana ta baiwa dukkan ma'aikatan lafiyar kasar Sin lambar yabo saboda abin da ta kira gagarumar gudumawar da suka baiwa kasarta. (Ibrahim)