in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
"Al'ummar Afrika ta Kudu na nuna adawa da kyamar baki", in ji shugaba Zuma
2015-06-15 10:03:23 cri
Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya ce, al'ummar kasarsa sun nuna adawa da kyamar baki, yanzu kasarsa na dukufa ka'in da na'in wajen kyautata dangantakar sada zumunta da sauran kasashe.

Shugaban ya bayyana hakan ne jiya a gun taron koli na kungiyar AU karo na 25 da ke gudana yanzu haka a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu.

Shugaba Zuma ya ce, al'ummar kasarsa sun nuna tsayyayiwar adawa ga nuna kyamar baki, aika-aikar da wasu tsirarrun mutane suka aikata ba zai wakilci al'ummar Afrika ta Kudu da yawansu ya kai sama da miliyan 50 ba, Afrika ta Kudu na kokarin kawo karshen yaki da aikata laifuffuka, don tsaron kasar da kare dukiyoyin jama'a.

A karshen watan Maris zuwa karshen watan Afrilun wannan shekara ce, aka samu barkewar rikicin nuna kyamar baki a biranen Johannesburg da Durban, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar murtane 7, tare da jikkatar wasu sama da 100, baya ga wasu miliyoyin baki suka bar gidajensu, kana aka wawushe daruruwan shaguna na baki.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China