in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Botswana ta ce ba ta da shirin aikewa da dakaru Nigeria
2015-01-20 14:12:58 cri

Kakakin gwamnatin kasar Botswana Jeff Ramsay ya fada a cikin wata sanarwa cewar, kawo ya zuwa yanzu gwamnatin Botswana ba ta da wani shiri na aikewa da sojojinta zuwa Nigeria, a sakamakon kiran da kungiyar hadin kan Afrika AU ta yi a kan kasashen dake cikin kungiyar da su taimakawa Nigeria da dakaru domin tunkarar hare-haren kungiyar tsagera ta Boko Haram.

A cikin wata sanarwa a makon da ya shude, shugabar kungiyar hadin kan Afrika Nkosazana Dlamini-Zuma ta bayyana cewar, akwai bukatar gaggawa ta samun taimakon kasashen Afrika da na duniya baki daya wajen tunkarar kungiyar 'yan ta'addan, musamman da yake ta'addanci na dakile shirin zaman lafiya na yankuna

Darektan kula da baki da hulda da jama'a na rundunar tsaro ta Botswana, Tebo Dikole ya ce, rundunar tsaro ta Botswana tana yin biyayya ga dokar rundunar tsaron kasar, kuma hakan na nufin suna amfani da umurnin babban kwamandan sojojin kasar shugaba Ian Kama.

Dikole ya kara bayyana cewar, zai yi wuya Botswana wacce ke cikin kungiyar raya kasashe ta kasashen kudancin Afrika SADC ta taka rawa a ayyukan kiyaye zaman lafiya a Nigeria saboda ko kadan ba ta cikin kungiyar tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China