in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harajin da hukumar kwastan ke tarawa a kasar Sin zai ci gaba da kasancewa cikin managarcin yanayi
2015-06-18 19:38:03 cri
Kakakin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin Shen Danyang, ya bayyana cewa bayan shigar kasar Sin kungiyar kasuwanci ta duniya ta WTO, a yanzu wa'adin kariyar da ake baiwa harajin kwastan na shekaru 15 na dab da karewa, wato a ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa. Bayan wannan lokaci, ana sa ran harajin kwastan na kasar Sin zai ci gaba da kasance cikin managarcin yanayi.

A yayin taron manema labarai da aka gudanar ma'aikatar kasuwancin kasar ta Sin, Mr. Shen ya bayyana ra'ayinsa dangane da wasu rade-radi dake nuna cewa farashin hajojin da ake shigo da su daga ketare zai ragu sosai, da zarar an kawo karshen wannan wa'adi na tsarin haraji, ya na mai cewa Sin ta shiga kungiyar WTO ne a ranar 11 ga watan Disambar shekarar 2001, kana ta fara rage harajin kwastan din ta daga dukkan fannoni a ran 1 ga watan Janairun shekarar 2002, inda ta gudanar da wannan aiki bisa matakai goma, kuma ta kammala galibin su a ran 1 ga watan Janairun shekarar 2005. Kaza lika ya zuwa ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2010, kasar ta Sin ta cika alkawarin da ta dauka dangane da rage harajin kwastan, kan dukkanin hajoji.

Bisa hakan ne kuma Mr. Shen, ya ce farashin hajojin da za a shigo da su daga ketare zuwa Sin ba zai ragu sosai ba, a gabar da za a kawo karshen wa'adin tsarin kariya kan harajin kwastan a kasar ta Sin a hukunce. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China