in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WTO ta zartas da yarjejeniyar sassauta sha'anin cinikayya
2014-11-28 16:08:50 cri
A jiya Asabar 27 ga watan nan ne kungiyar cinikayya ta duniya WTO ta sanar da zartas da yarjejeniyar kawo sassauci ga harkokin cinikayya, wadda aka kwashe watanni hudu ana tattauna shiryawa.

An dai gabatar da wannan sanarwa ne yayin taron musamman na majalisar zartaswar kungiyar.

A watan Satumbar bara ne dai kungiyar WTO ta kulla yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban a karo na farko, na yarjejeniyar birnin Bali, a taron ministocin kungiyar karo na tara, yarjejeniyar da ta tsara samar da saukin cinikayya wadda kuma ta ba da babbar gudummawa kan cinikayyar kasa da kasa.

Wannan yarjejeniya baya ga kasancewar ta hanyar kawo sauki ga cinikayya tsakanin kasa da kasa, a daya hannun kuma ta rage yawan kudaden da ake kashewa kan hakan. Da samar da karin guraben aikin yi, da kuma kara yawan kudin cinikayyar kasa da kasa.

Bisa yarjejeniyar an bayyana cewa ranar 31 ga watan Yuli, ita ce rana ta karshe a matakain farko na yarjejeniyar, koda yake kungiyar ba ta iya gudanar da ayyukan dake kunshe cikin yarjejeniyar yadda ya kamata ba, bisa wannan lokacin da aka tsara.

Game da wannan batu babban sakataren kungiyar ta WTO Roberto Azevedo, ya bayyana cewa bayan zartas da yarjejeniyar samar da saukin gudanar da ciniki a wannan karo, mambobin kungiyar za su fara gudanar da bincike kan yarjejeniyar bisa tsarinsu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China