Amina wadda 'yar asalin kasar Kenya ce, kuma kwararriyar ma'aikaciyar Diflomasiyya, ta shaidawa kamfanin dillancin labaru na kasar Sin Xinhua cewa, matakin kammala batutuwan da aka fara tattaunawa a taron na Doha, zaimakawa wajen samar da daidaito, da habakar tattalin arzikin kasashen duniya baki daya, baya ga samar da karin arziki da yalwa da tace hakan zai haifar.
Amina dake wannan tsokaci yayin da take halartar taron kungiyar AU karo na 20 dake gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, na burin samun karin goyon baya daga wakilan kasashen Afirka, dama na ragowar kasashen duniya dake halartar taron.
Muddin dai ta kai ga cimma nasarar samun wannan mukami, za ta kasance mace ta farko, muka 'yar Afirka ta daya da ta taba jagorantar kungiyar ta WTO.(Saminu)