Rahoton ya kuma yi hasashen cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kasancewa kan gaba, wajen samun bunkasuwar tattalin arziki cikin shekarar da muke ciki, wanda hakan zai bata damar shigo da hajoji daga kasashen ketare, sai dai yanayin tawayar bukatun kasuwannin kasahen Turai a hannu guda, zai rage fitar hajojin Sin zuwa kasashen ketare.
Babban sakataren kungiyar cinikayya ta duniya Pascal Lamy, ya yi kira ga kasa da kasa, da su mai da hankali kan karfafa tsarin cinikayyar dake tsakanin bangarori da dama, don kada a fada yanayin neman kariya, daga karayar tattalin arziki. Ya kuma nuna cewa, cinikayya tsakanin kasa da kasa, na iya sake bunkasa tattalin arzikin duniya, da kuma goyon bayan ci gaba a tsawon lokaci nan gaba. (Maryam)