in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bayyana rashin jin dadinta game da hukuncin da WTO ta yanke kan albarkatun kasa
2014-08-08 10:33:48 cri
Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayyana takaicinta game da shawarar da kungiyar cinikayya ta duniya (WTO) ta yanke wadda ta kai ta ga yanke hukunci kan yadda Sin ke fitar da albarkatun kasa zuwa ketare.

Wani jami'in ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya ce, hukuncin da kungiyar cinikayya ta duniya ta yanke kan wannan sha'ani ya sabawa dokokin kungiyar da kuma tanade-tanaden Sin na shiga wannan kungiyar. Jami'in ya ce, Sin ta yi maraba da shawarar da kungiyar ta yanke, matakin da zai taimaka wa Sin daukaka kara, a hannu guda kuma ba ta goyi bayan karar da Amurka ta shigar bayan yanke wannan hukunci ba.

A watan Maris ne kungiyar ta WTO ta yanke hukunci cewa, Sin ba ta bi dokokin kungiyar sau da kafa game da fitar da nau'o'in albarkatun kasa zuwa ketare, lamarin da ya sa a watan Afrilu Sin ta daukaka kara game da hukuncin da WTO ta yanke kan wannan sha'ani.

A watan Maris na shekarar 2012, kungiyar tarayyar Turai da kasashen Japan da Amurka suka hada kai wajen shigar da kara gaban kungiyar WTO game da matakan Sin na fitar da nau'o'in albarkatun kasa zuwa ketare, inda suke ikirarin cewa, an takaitawa wasu kasashe amfana da irin wadannan albarkatu, lamarin da ya baiwa Sin damar yin gogayya fiye da wasu.

Kasar ta bayyana kudurinta na nazartar wannan hukunci da idon basira, tare da daukar matakai kamar yadda dokokin WTO suka tanada don kiyaye damar yin gogayya da tabbatar da ci gaba mai dorewa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China