in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana na mai goyon bayan Kyerematen ya zamo shugaban hukumar WTO
2013-03-02 16:31:16 cri
Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya yi bayani ranar Jumma'a cewa, wanda kungiyar hada kan kasashen Afirka AU ta zabo, John Alan Kwadwo Kyerematen don samun matsayin darekta janar na hukumar cinikayya ta duniya WTO, ya cancanci samun wannan matsayin.

Ya bayyana hakan ne bayan dawowarsa daga wata ganawa ta kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma ECOWAS wanda aka yi a Kwadibwa.

Kyerematen wanda ya taba hawan mukamin ministan cinikaya da masana'antu a kasar Ghana da kuma jakadan kasar a kasar Amurka, a halin yanzu dai shi ne shugaban cibiyar manufofin harkar cinikayya na Afirka karkashin hukumar tattalin arziki ta MDD a Afirka (UNECA) dake birnin Addis Ababa, kasar Habasha.

Kungiyar ta AU ta zabe shi ya yi takarar wannan mukami ne yayin wata ganawar da aka yi a birnin Addis Ababa a cikin watan Yuni shekarar 2012 kuma ya samu goyon bayan kasashen yankunan Pasifik da Carribean na Afirka.

Wa'adin darekta janar na hukumar cinikayya ta duniya Pascal Lamy, wanda dan kasar Faransa ne zai kare a cikin watan Satumba shekarar 2013.

Shugaban Ghana ya ci gaba da cewa, shi Kyerematen ya taba rike mukamin ministan cinikayya a kasar Ghana, ko shakka babu ya cancanci matsayin don haka za su yi bakin kokarinsu don ganin ya samu wannan mukamin.

Ya ce ba'a taba samun wani dan Afirka a matsayin darekta janar na hukumar cinikayya ta duniyan ba, don haka yake ganin idan aka nada dan Afirka bisa la'akari da matsalolin tattalin arziki a duniya, zai taimakawa kasashen Afirka da ma Ghana. (Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China