Ya yin zaman na wannan lokaci, bangarori daban daban sun za su ci gaba da gudanar da shawarwari, kan shirin cimma sabuwar yarjejeniyar sauyin yanayi a karshen shekarar bana, tare da kara azama a fannin tinkarar kalubalen sauyin yanayi kafin nan da shekarar 2020 da dai sauransu.
Ana fatan ci gaba da gudanar da shawarwarin har zuwa ranar 11 ga wata, kana daya daga cikin manyan batutuwan da za a maida hankali a kan su, sun hada da batun takaita abubuwan dake cikin shawarwari, game da yarjejeniyar yanayin duniya, wadda aka tabbatar a birnin Geneva na kasar Switzerland a cikin watan Febrairun da ya shude.
Bisa tsarin shirin, za a zartas da sabuwar yarjejeniyar yanayin duniya, bisa tushen takaitar shawarwari a babban taron sauyin yanayi na MDD, wanda ke tafe cikin watan Disambar bana, a birnin Paris na kasar Faransa. Kudurin da kuma za a aiwatar tun daga shekara ta 2020, zai zamo ma'aunin fitar da iska mai dumama yanayi, da kuma batun tinkarar sauyin yanayi bayan shekarar 2020. (Zainab)