Jami'an biyu sun bayyana hakan ne cikin sakonsu a ranar muhalli, wadda a bana ke da taken "Kara kira, ga magance dagawar teku".
A jawabinsa Ban Ki-moon ya ce, babban taron MDD ya sanar da shekarar 2014 a matsayin shekarar kananan kasashe dake tsibirai masu tasowa. Hakazalika Ban Ki-moon ya bayyana cewa, kananan kasashen dake tsibirai na fuskantar kalubale da dama, kamar ambaliyar ruwa ta tsumani, da dagawar teku, kuma da dama daga cikinsu ba su da cikakken karfi na tinkarar sauye-sauyen yanayi. Ban ya yi kira da a sa lura ga mawuyacin halin da irin wadannan kasashe ke fadawa, tare da samar da dabarun tinkarar sauye-sauyen yanayi, da inganta karfinsu wajen kare muhalli, da kuma samun bunkasuwa mai dorewa a nan gaba.
Mr. Ashe ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, bisa nazarin da aka yi, ya zuwa shekarar 2100, mai yiwuwa ne dagawar da teku ke yi zai karu da mita biyu sakamakon dumamar yanayi, wanda zai hana mutane iya zama a kananan kasashe dake tsibirai, musamman ma kasashen dake yankin tekun Pasific.
Don haka idan ana fatan tabbatar da samun wadatar irin wadannan kasashen a nan gaba, ya zama wajibi a raya su, tare da daukar matakan bunkasuwarsu ba tare da gurbata muhalli ba. (Zainab)