in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa: Kada a dora muhimmanci kan rage fitar da gurbatacciyar iska kawai a taron yarjejeniyar sauyin yanayi na Paris
2015-05-19 14:21:42 cri

Ministan harkokin wajen kasar Faransa kuma shugaban kungiyar kasashen da suka kulla yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 21 wato taron Paris, Laurent Fabius ya bayyana a kasar Jamus a jiya Litinin cewa, an yi hasashe cewa, ya kamata yarjejeniya game da matsalar yanayin duniya da za a kulla a birnin Paris ta kunshi batutuwa da yawa, kana kamata ya yi a dora muhimmanci kan sabawa da sauyin yanayi kamar yadda aka yi kan batun rage fitar da iska mai dumama yanayi.

Laurent Fabius ya bayyana a yayin da yake halartar taron musayar ra'ayi kan sauyin yanayi na st.Petersberg da gwamnatin Jamus ta kira a wannan rana cewa, matsalar sauyin yanayi ta hana bunkasuwar kasashe da dama, musamman ma kasashen Afrika da wasu kananan tsibiran kasashe. Sabo da haka, yadda za a saba da batun sauyin yanayi zai zama daya daga cikin batutuwan da aka tabo a cikin sabuwar yarjejeniyar.

A shawarwarin da aka yi a baya, wasu kasashe masu ci gaba sun jaddada nauyin da ya rataya a wuyan kasashe masu tasowa na rage fitar da gurbattaciyar iska, musamman ma neman kasashen Sin da India da sauran kasashe masu tasowa su dauki nauyin rage fitar da gurbatacciyar iska, wannan ya sa ba a iya samun cigaba ba a gun taron shawarwarin yanayi.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China