in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afrika sun yi alkawarin zuba jari kan sauyin yanayi
2015-04-28 10:37:33 cri

Kasashen Afrika na yankin kudu da hamadar Sahara za su mai da yawancin jarinsu a kan ayyukan da zai karbi sauyin yanayi da ake fama da shi yadda za'a yi saurin inganta kyautatuwar muhalli, in ji wassu jami'ai.

Da suke magana a taron kasa da kasa a Nairobin Kenya, game da yadda kasashe za su rungumi irin wadannan ayyukan, masu ruwa da tsaki da kuma masana sun jaddada samar da kudi a wannan bangaren cewa, zai ba da damar da za'a iya tunkurar duk wani irin sauyin yanayi da ka iya tasowa.

Babbar sakatariyar ma'aikatar muhallin Kenya, Judi Wakhungu ta ce, rashin iassun kudade da fasaha, sannan da tazarar ilimi a wannan bangaren sun sa kasashen Afrika ke wahala wajen jure wa sauyin yanayi. Ta ce, kasashen Afrika sun amince da daukan manyan matakai don samun kwarin gwiwwar yaki da sauyin yanayi da ake dora laifin a kan tsananin talauci, yaduwar kwayoyin cuta da rikice rikice a wuraren da ake samun albarkatun kasa.

Hukumomi da dama sun mai da hankali a kan samar da isassun kudade a wannan bangaren a yankunan Saharan Afrika domin ba da damar jure wa yawan samun fari a wurare, karancin ruwa, da tabarbarewar muhalli.

Babban masanin tattalin arziki a bankin raya kasashen Afrika wato ADB Tom Owiyo ya bayyana cewa, hukumomi masu ba da taimako sun kara adadin kudi a bangaren da ya shafi yanayi a Afrika.

Hukumomin da dama a shekara ta 2013 sun amince da samar da kudi har dala miliyan 952 domin taimakawa ayyuka a bangaren sauyin yanayin a yankunan hamadar Afrika, sannan cewar Owiyo, bankin na ADB ya ba da nasa gudunmuwar kudi dalar Amurka 432 da niyyar inganta ayyukan zuba jari da suka shafi ba da kwarin gwiwwa a wannan bangaren.

Yana mai cewa, zuba jari a bangaren samar da kwarin gwiwwa a gabashin Afrika ya samar da moriya ta tattalin arziki da muhalli. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China