Za a kwashe kwanaki 6 ana gudanar da shawarwarin, da nufin aiwatar da sakamakon da aka cimma wajen taron yanayin da ya gudana a karshen shekarar bara a birnin Lima na kasar Peru. Mahalartan taron za su takaita kundin yarjejeniyar da aka kulla a taron Lima dake dauke da shafuna 37, ta yadda za a samu wani sabon daftarin kundin yarjejeniyar kafin watan Mayu mai zuwa.
Duk da cewa lokaci ya kure domin a share fagen kulla wata sabuwar yarjejeniya a taron Paris, amma har yanzu akwai sabanin ra'ayi tsakanin kasashe masu sukuni da wadanda tattalin arzikinsu ke tasowa, kan yaya za a raba nauyin da ya kamata a sauke wajen rage fitar da iska mai dumama yanayi, da yawan kudin tallafin da ya kamata kasashe masu sukuni su baiwa kasashe masu tasowa, da dai sauran manyan batutuwa. A halin yanzu yarjejeniyar Tokyo ita kadai ke kayyade yawan iska mai dumama yanayi da ya kamata a rage fitarwa, wadda kuma wa'adinta na 2 zai cika nan da shekarar 2020. (Bello Wang)