Sakatare janar na MDD, mista Ban Ki-moon ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da ta kara karfafa kokarinta domin rage kashe itatuwa a cikin dazuzzuka a duniya, kiyaye dazuzzuka a cikin yanayi mai kyau da kuma samar da dukkan matakan da suka wajaba domin fuskantar canjin yanayi. Mista Ban ya fadi hakan a cikin wata sanarwar da aka fitar albarkacin ranar dazuzzuka ta kasa da kasa da ake gudanar da bikinta a 21 ga watan Maris kowace shekara. Kimanin mutane biliyan 1.6 kuma daga cikinsu wasu fiye da 2000 na kabilu mazauna wurin ke samun abincinsu, itatuwan girki, itatuwan bukatunsu da ma kudin shiga daga gandun daji. Kana kashi uku cikin kashi hudu na ruwan da ake samu suna fitowa daga wadannan yankunan dazuzzuka. Dazuzzuka suna taimakawa wajen hana zabtarewar kasa da fari, kuma a locakin ambaliyar ruwa itatuwa suna taimakawa wajen rage asarar rayuka da dukiyoyin jama'a, in ji mista Ban Ki-moon a cikin wannan sanarwa.
Inda ya kara da cewa, dazuzzuka nada babban matsayi a cikin shirin bunkasuwa na bayan shekarar 2015. Haka kuma suna taka muhimmiyar rawa bisa karfinsu na jurewa ayyukan da ke janyo sauyin yanayi, in ji mista Ban tare da nuna cewa sauye sauyen yanayi sun kasance taken ranar dazuzzuka ta kasa da kasa na wannan shekara. (Maman Ada)