Wannan yarjejeniya zata kasancewa babban buri da tilastawa domin aiwatar da ita yadda ya kamata da kuma kan yadda za'a fuskanci babban kalubalen da sauyin yanayi ke janyowa, in ji Jean Claude Nduwayo, ministan muhallin kasar Burundi, a yayin bikin rufe taron kara wa juna sani da ya gudana a wannan makon a birnin Bujumbura, wanda ya samu halartar wakilan kasashen Rwanda, Kamaru, Togo, Gabon, Afrika ta Tsakiya, Congo, Chadi, Guinee-Equatoriale da Sao Tome da Principe.
Wadannan kasashe sun kuma alkawarta maida hankali kan abubuwan dake damuwar tsakiyar yankin Afrika musammun ma kan batun kashe itatuwa ta yadda za'a cimma wani cigaba mai karko.
Haka kuma mahalarta taron sun dauki niyyar tashi tsaye tamkar tsintsiya a yayin wannan dandalin kasa da kasa na Paris (COP 21), ta hanyar kira da a kara karfafa alkawuran da kasashe da suka dauka ta fuskar rage abubuwan da ke janyo dumamar yanayi da kuma fuskantar kalubalolin canjin yanayi da samar da kudade. (Maman Ada)