Ministoci da kwararru daga kasashen Afirka sama da 50, sun fara taron lalubo hanyoyin magance matsalar sauyin yanayi a birnin Alkahira na kasar Masar.
Taron wanda aka bude a jiya Laraba, ya samu halartar firaministan Masar Ibrahim Mahlab, da kuma shugaban zaman na wannan karo, kuma ministan muhallin kasar Khaled Fahmy.
Rahotanni sun bayyana taron a matsayin wani bangare na taro karo na 15, na dandalin tattaunawar ministocin nahiyar game da muhalli ko AMCEN a takaice.
Gabanin bikin bude taron, firaminista Mahlab ya shaidawa mahalartan sa cewa, taron na wannan lokaci ya zo a gabar da ake da matukar bukatar mai da hankali, ga tsara manufofin da suka dace, domin sauke nauyin dake wuyan gamayyar kasashen Afirka, wajen dakile matsalar sauyin yanayi. Hakan ya kuma dace da manufar cimma nasarar yarjejeniyar kasa da kasa da ake fatan amincewa da ita nan da karshen wannan shekara.
Ana dai sa ran za a nazarci batun yadda za a sakawa nahiyar Afirka, a matsayinta na nahiyar da ta fi fuskantar matsalar da sauyin yanayi ke haifarwa.
Binciken baya bayan nan da shirin MDD mai kula da muhalli ya fitar ya nuna cewa, matakan daidaita matsalar sauyin yanayi a Afirka za su lashe zunzurutun kudi har dalar Amurka biliyan 50 a kowace shekara, nan da tsakiyar wannan karni da muke ciki. (Saminu)