Mr. Hong ya ce rahoton dake kunshe da wannan aniya ta Amurka, ya nuna burin kasar na dinke barakar dake tsakaninta da Cuba. Matakin da kuma zai taimaka matuka, wajen inganta kudurin kasashen biyu na sake dawo da dangantakar diflomasiyya mai dorewa.
Mr. Hong wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labaru da ya gudana a nan birnin Beijing, ya kara da cewa Sin na fatan ganin Amurka ta dage takunkumin da ta sanyawa Cuba, matakin da zai taimakawa bunkasar kasashen biyu, da al'ummunsu, da ma burin wanzar da zaman lafiya da ci gaban yankin da suke.
Kasar Cuba dai ta kasance cikin jerin kasashen da Amurka ke kallo, a matsayin masu goyon bayan ta'addanci a duniya tun cikin shekarar 1982. Sauran kasashen dake kan wannan layi su ne Iran, da Sham, da kuma Sudan. (Saminu Hassan)