Kasar Sin ta kakkausa murya wajen yin Allah-wadai, da harin da aka kai jami'ar Moi da ke garin Garissa na kasar Kenya, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 147, a cewar madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin.
Madam Hua ta bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa. Ta kuma mika sakon ta'aziyya ga wadanda suka rasa rayukansu yayin harin, tare da jajantawa iyalan mamatan, da kuma wadanda suka jikkata sakamakon harin.
Kakakin ta jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka, wajen mara wa Kenya baya, a kokarinta na kiyaye tsaron kasa, da kuma wanzar da yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da take baki daya. (Tasallah Yuan)