in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta tsaurara matakan tsaro a kan iyakar ta da Somaliya
2015-04-02 21:36:05 cri
Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya, ya ce jami'an tsaron kasar sa, sun kara tsaurara matakan tsaro a kan iyakar kasar da Somaliya, biyowa bayan harin da mayakan kungiyar Al-Shabab suka kaddamar kan wata jami'ar kasar Kenya dake garin Garissa.

Shugaba Kenyatta wanda ya bayyana hakan cikin wata nasarwar da aka fitar a birnin Nairobi, ya kuma yi kira da al'ummar kasarsa da su kara lura, musamman a wannan lokaci da hare-haren ta'addanci ke karuwa.

Rahotanni dai na cewa ya zuwa yanzu, adadin wadanda suka rasa rayukansu yayin harin sun kai mutane 17, baya ga wasu da dama suka jikkata.

Jami'an tsaron kasar dai sun yi musayar wuta da maharan wadanda suka rufe fuskokinsu, bayan sun kai hari jami'ar tare da yin garkuwa da wasu daga daliban jami'ar. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China