Rahotanni sun tabbatar da rasuwar 'yan sanda 2 da kuma farar hula guda, ya yin harin na ranar Juma'a, a wani wuri kusa da inda mayakan kungiyar suka hallaka mutane 28 cikin watan Nuwambar bara.
Jami'an tsaron yankin dai sun ce gwamnan ya tsallake rijiya da baya, ba tare da samun koda kwarzane ba. Ba dai wannan ne karon farko da aka kaiwa Ali Roba hari ba, an ce a wannan lokaci gwamnan na kan hanyar sa ce zuwa garin Wargadud dake yankin Elwak domin halartar wani taro. Kuma maharan sun yi amfani ne da wata roka inda suka harba gurneti kan tawagar gwamnan.
Da ma dai wannan wuri ya sha fuskantar hare-hare daga mayakan Al-Shabaab, kasancewar sa kusa da yankunan kasar da yaki ya daidaita. An ce maharan kungiyar kan tsere zuwa kan iyakar kasar da kasar Kenya, da zarar sun kaddamar da irin wannnan hari.
Rahotanni sun ce harin da aka kaiwa Ali Roba, ya zo 'yan kwanaki, bayan da dakarun Amurka sun hallaka daya daga wadanda ake zargi da kaddamar da harin Westgate a kasar Kenya, ta wani harin sama da dakarun Amurkan suka kaddamar ranar Laraba a kasar Somalia.