in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 15 sun rasu sakamakon harin da aka kai wa wata jami'ar kasar Kenya
2015-04-02 19:31:23 cri
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar daga garin Garissa dake arewa maso gabashin kasar Kenya, an ce, yawan mutanen da suka rasu ya karu zuwa 15, baya ga wasu mutane 65 suka jikkata, sakamakon wani harin da aka kai wata jami'ar kasar Kenya dake garin na Garissa.

Mr. Adan Duale, shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin kasar Kenya ya tabbatar da wannan adadi, inda ya kara da cewa, har yanzu rundunar kwantar da tarzoma ta kasar na aikin ceton sauran daliban da aka ritsa yayin harin.

An labarta cewa, kungiyar Al-Shabaab ta kasar Somaliya ce ta kaddamar da wannan hari. Tuni dai kungiyar ta bayyana cewar ta riga ta hallaka dalibai da dama 'yan Kenyan, kuma za ta ci gaba da kai hari kan 'yan Kenya dake jami'ar, cikin wani sako da ta fitar ta kafar rediyon ta. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China