Karamin jakadan ofishin jakadancin Sin dake kasar Kenya Yao Ming, da Zhu Min, babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da ke jami'ar DongHua, da Mandaga, gwamnan jihar Uasin Gishu, gami da Mibe, shugaban jami'ar Moi sun halarci bikin bude kwalejin.
Bangarorin biyu sun yi imani cewa, a karkashin hadin gwiwa daga gwamnatocin kasashen biyu da masana'antunsu, kwalejin confucius ta jami'ar Moi za takawo babbar dama ga sana'o'in masaku a kasashen, da kara dankon zumunci a tsakaninsu.
Wani jami'in kwalejin confucius na jami'ar Moi ya ce, bayan da aka kafa kwalejin confucius, za akokarta wajen yada harshen Sinanci, da yalwata al'adun dinkin tufafi da fasahohin masaku na Sinawa, ta yadda za a sa kaimi ga ci gaban sana'ar masaku a kasar Kenya.(Bako)