Brown ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a cibiyar MDD dake birnin New York a wannan rana cewa, a cikin shekaru biyar da suka wuce, yawan hare-haren da aka kai kan makarantu a sassan duniya ya zarce dubu 10, kuma kananan yara miliyan 28 ba sa iya zuwa makarantu a yankunan da ke fama da rikice-rikice da yanayin dokar ta baci.
Kana Brown ya bayyana cewa, kasashen Nijeriya, Pakistan da sauran kasashe suna hadin gwiwa tare da hukumomin duniya kamar MDD wajen kara azama ga kiran tabbatar da tsaron makarantu, tare da tabbatar da ganin kananan yara sun je makaranta ta hanyar kai dalibai yanki mai tsaro, kafa makarantu masu tsaro, kara daukar matakai a yayin da aka shiga halin dokar ta baci da dai sauransu. Kana Brown ya bukaci da a gudanar da wannan kira a kasashen Lebanon, Sudan ta Kudu, Congo Kinshasa da sauran kasashen duniya. (Zainab)