Mr. Ban wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, wadda ita ce ranar gandun daji ta duniya, ya kara da cewa sayar da gandun daji ba bisa ka'ida ba, laifi ne dake shafar kasashe daban daban. Kana daukar matakai kan hakan yana da muhimmancin gaske, wajen bada kariya ga gandun daji, da tabbatar da samun ci gaba mai dorewa. Ya ce hakan zai magance irin laifukan da ke illata zaman lafiya da tsaro, a yankunan dake fama da rikice-rikice.
Haka zalika, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, ana yin amfani da albarkatun gandun daji a fannonin samar da magani, da abinci, da kayan gine-gine, da kayayyakin gida, da kayan kwalliya, da tufafi da dai sauransu, don haka akwai bukatar masu samar da irin wadannan kayayyaki, da masu sayen kayayyakin daga bangarori daban daban na al'ummomin kasashen duniya, su goyi bayan yaki da laifukan da suka jibanci gandun daji.
Har wa yau Mr. Ban na ganin ya zama tilas masu yaki da laifuka a wannan fanni, su samu amincewa daga bangarorin al'ummu daban daban, kana dukkan kamfanoni, da jama'a za su iya taka muhimmiyar rawa a wannan fanni. (Zainab)