Taron dai wanda ya gudana a jiya Juma'a na zuwa ne gabanin ranar mata ta duniya dake tafe ran 8 ga watan nan na Maris.
Cikin jawabin da ya gabatar yayin zaman, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon, ya ce bana shekara ce ta cika shekaru 20 da babban taron mata na kasa da kasa na Beijing, kuma cikin shekaru 20 da suka gabata, shigar mata cikin harkokin siyasa, da fannonin ilimi, da kuma samun ayyukan yi na ci gaba da samun kyautatuwa.
Ya ce yanzu haka wasu kasashe na kafa dokoki na musamman, domin kawar da nuna wariya ga mata, da na warware matsaloli masu nasaba da muzgunawa mata, sai dai a wasu kasashe ba a samu ci gaba yadda ya kamata ba, musamman a fannin ci gaban ilimin mata, da na adalci tsakanin mata da maza, da kuma bangaren baiwa mata iko.
Mr. Ban ya kuma kara da cewa, kamata ya yi gamayyar kasa da kasa su amince da bambancin dake akwai tsakanin kasashen duniya game da wannan aiki, da kuma tabbatar da ci gaban aikin a nan gaba.
Bugu da kari shugaban babban taron MDD Sam Kahamba Kutesa, ya ce kamata ya yi a gudanar da karin shawarwari, tare da daukar matakai yadda ya kamata, domin warware matsalar nuna wariya ga mata, da kuma cimma burin da aka sanya gaba na samar da dauwamammen ci gaba. (Maryam)