An dai gudanar da cikakken zama na babban taron MDD karo na 69 a jiya Alhamis, inda aka cimma daidaito, tare da zartas da wani kuduri na gudanar da taron musamman, game da tunawa da cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin da aka yi da manufar fascist a watan Mayun bana.
Bayan da aka zartas da kudurin, Liu Jieyi ya bayyanawa 'yan jarida cewa, bisa shawarar kasar Sin, an gudanar da muhawara kan tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasa da kasa a ranar 23 ga wata a birnin New York, a karkashin jagorancin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi. Muhawarar ta kuma samu goyon baya sosai daga wajen kasashe mambobin kwamitin sulhun MDDr.
A cewarsa gudanar da muhawarar na alamta kiran da aka yiwa kasashe membobin kwamitin sulhun, na koyi daga fasahohin da aka samu a baya, da nanata cika alkawarin bin ka'idojin kundin tsarin MDDr, da kuma neman hanyoyi mafiya dacewa, wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya a sabon halin da ake ciki. (Zainab)