in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron farko na ministocin BRICS da UNESCO a Paris ya mai da hankali kan ilmi
2013-11-06 14:22:30 cri

Zaman taron farko na ministocin BRICS da UNESCO kan ba da ilmi ya gudana a ranar Talata a cibiyar kungiyar UNESCO dake birnin Paris na kasar Faransa tare da halartar manyan jami'ai a fannin ba da ilmi na kasashen BRICS.

Zaman taron ministocin BRICS da UNESCO, an shirya shi ne bisa tunanin kungiyar UNESCO da Afrika ta Kudu dake shugabantar kungiyar BRICS a wannan karo domin aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron shugabannin BRICS.

Wannan ganawa na mai da hankali kan hadin gwiwar kasashen BRICS a fannin ba da ilmi da kuma karfafa yin musanyarsu tare da kungiyar UNESCO domin fadada hadin gwiwar bangarorin biyu yadda ya kamata bisa ajandar bunkasuwa ta gabanin shekarar 2015 kan ba da ilmi a duniya.

A cewar ministan ba da ilmi na kasar Sin Yuan Guiren, kasashe biyar na BRICS da suka hada da Rasha, Indiya, Sin, Brazil da Afrika ta Kudu suna tunkarar ayyukan dake gaban su kamar batun gaggauta samun cigaba, muhimmancin samar da alheri da jin dadi ga jama'ar wannan gamayya. Tabbatar da cimma wadannan muradu na da nasaba da kyautatuwar ingancin hanyar ba da ilmi, in ji mista Yuan Guiren. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China