Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin ya yi bayani kan kudurin tunawa da cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin duniya na biyu na MDD
Jiya Asabar 27 ga wata, babban taron MDD karo na 69 ya kira cikakken zaman taronsa, inda aka cimma ra'ayi daya kan zartas da daftarin kudurin tunawa da cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin duniya na biyu, wanda kasar Sin, kasar Rasha da wasu kasashe gaba daya sama da 80 suka gabatar da shi. Bisa wannan kuduri, an jaddada cewa, yakin duniya na biyu ya haddasa babbar illa ga mutanen duniya, musamman ma ga jama'ar kasashen Asiya da Turai, kuma an tsaida kudurin kira taron musamman na tunawa da cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin duniya na biyu na babban taron MDD.
Dangane da lamarin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a ran 28 ga watan Fabrairu cewa, kasar Sin na fatan bangarorin da abin ya shafa sun yi amfani da wannan dama domin koyon darussan tarihi, da kuma kafa makoma mai haske, neman hanyoyin da suka dace domin kiyaye zaman lafiya da tsaron kasa da kasa cikin sabon yanayin nan da muke ciki. (Maryam)