in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare janar na MDD ya kaddamar da sabuwar manufa ta ilmi tare da samun cikakken goyon bayan kasashen duniya
2012-09-27 10:47:21 cri

A ran Laraban nan ne sakatare janar na MDD Ban Ki-Moon ya kaddamar da wata sabuwar manufa ta ilmi mai samun karbuwa tsakanin kasashen duniya baki daya, wacce ke da nufin sa ilmi kan gaba don a samu gaggarumin ci gaba wajen cimma burin muradin karni musamman ma a fuskar ilmi.

Yayin kaddamar da manufar mai take "ilimi shi ne kan gaba", Mr Ban ya ce, manufarmu iri daya ce, domin burinmu shi ne mu ga cewa, 'ya'yanmu sun samu ilmin firamare sun kuma wuce zuwa manyan makarantu don samun ilmi da zai taimaka masu su cimma nasara a rayuwarsu.

Cimma manufar samar da ilmin firamare a duniya baki daya muhimmin sashe ne na muradun karni, dake cikin matakai 8 na yakin kawar da talauci nan da shekara ta 2015.

A ran Larabar ne a kaiwa sakatare janar din alkawarin dalar Amurka biliyan 1.5 don gabatar da sabuwar manufar.

Sabuwar manufar na mai kokarin jan hankali abokan tafiya, tsoffi da sabbabi don a samu cimma samar da ilmin firamare a fadin duniya kafin ma shekara ta 2015 din da aka yanka na muradin karni.

Ana bukatar karin kudi da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 2.4 don a samu cike gurbi musamman ma na yaran makarantun firamare da karamar makarantar sakandare.

A karshen shekarun 1990, a kalla yara 'yan shekarun karatun firamare guda miliyan 108 ne ba'a sa a makaranta ba, inda yanzu haka wannan adadi ya yi kasa zuwa miliyan 61, haka kuma rata dake tsakanin yawan yara maza da yara mata da ake sa su a makaranta ya samu raguwa bisa rahoton sa ido na hukumar kula da ilmi, kimiyya da al'adu ta MDD wato UNESCO.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China