A cikin jawabinsa, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, tilas ne kasashen duniya su rika girmama tare da maida hankali ga rawar da mata ke taka wa, da samar da wata duniyar da ta dace, inda kowane mutum yake da hakkinsa na samun girmamawa. Kana ya yi kira ga mata da su taka muhimmiyar rawa a duniya.
Wani dalibin makarantar sakandare ya bayyana cewa, shi da abokan karatunsa sun shiga zanga-zangar ce, kuma a matsayinsu na matasa, suna goyon bayan ra'ayin samar da adalci ga mata. (Zainab)