Wang Yi ya kuma jaddada cewa, cikin shawarwarin da ake yi dangane da batun, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan neman hanyar zaman lafiya wajen warware matsalolin da abin ya shafa da kuma nuna adalci, inda ta ba da gudumawa yadda ya kamata cikin harkokin shiga tsakani. Haka kuma, kasar Sin tana son ci gaba da yin hadin gwiwa da bangarorin da batun nukiliyar kasar Iran ya shafa, ta yadda za a iya ci gaba da ba da gudumawa wajen warware batun nukiliyar kasar Iran cikin yanayi mai kyau. (Maryam)