Kana ya nuna cewa, kafa zamantakewar al'ummar kasa a dukkan fannoni na da ma'ana a fannoni guda hudu, da farko dai wannan aiki zai shafi dukkan jama'ar kasar Sin, da kuma dukkanin sassan kasar, na biyu za a tafiyar da ikon mulkin kasar ba tare da cin hanci da rashawa ba, na uku za a inganta karfin kasar, da kyautata zaman rayuwar jama'ar ta, na hudu za a tabbatar da adalci a shari'a da dokoki a kasar.
Sharhin ya nuna cewa, yayin da ake kokarin raya kasa daga fannoni hudu; wato kafa zamantakewar al'umma mai annashuwa da jituwa, da zurfafa yin kwaskwarima, da gudanar da harkokin kasa bisa dokoki, da daukar kyawawan matakan gudanar da harkokin jam'iyyar kwaminis ta kasar, kafa zamantakewar al'umma mai annashuwa da jituwa shi ne buri na farko da ake fatan cimma nasarar sa.
Har wa yau sharhin ya nuna cewa an yi amfani da aikin zurfafa yin kwaskwarima wajen warware manyan matsaloli yayin da ake raya kasar ta Sin, da tabbatar da zamanintar da kasar ta hanyar gudanar da harkokin kasar bisa dokoki, kana da dauki tsauraran matakai wajen gudanar da harkokin jam'iyya don zurfafa tushen gudanar da harkokin kasar, matakan da za su tallafa wajen kammala kafa zamantakewar al'umma mai annashuwa da jituwa yadda ya kamata. (Zainab)