in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zurfafa gyare-gyaren da kasar Sin ke yi a gida a dukkan fannoni zai samar mata karfin cimma burinta
2015-02-26 21:07:53 cri

A gobe ne jaridar People's Daily ta nan kasar Sin za ta fid da wani sharhi mai taken "Zurfafa gyare-gyaren da kasar Sin ke yi a gida a dukkan fannoni zai ba ta karfin cimma burinta ba tare da kasala ba".

Sharhin ya ce, muhimman bayanan da babban sakataren JKS. mista Xi Jinping ya yi dangane da yadda za a zurfafa yin gyare-gyaren da kasar Sin ke yi a dukkan fannoni sun mayar da "batun yin gyare-gyare a cikin gida" a matsayin harsashe, inda suka mai da hankali kan yadda za a zurfafa gyare-gyaren a dukkan fannoni.

Ya ce, ya zama dole mu gudanar da ayyukan gyare-gyaren bisa cikakken tsari. Kada mu kaucewa lamarin. Kamata ya yi mu kalli matsaloli baki daya. Haka zalika, wajibi ne a yi la'akari da dangantakar da ke tsakanin matakan yin gyare-gyaren. Burin kasar Sin na zurfafa yin gyare-gyare a cikin gida a dukkan fannoni shi ne raya kasar Sin ta gurguzu, wadda za ta kara samun karfi wajen ba da jagora.

Sa'an nan sharhin ya jaddada cewa, yayin da kasar Sin take yin gyare-gyare a gida a halin yanzu, baya ga daidaita kalubalen da take fuskanta, kamata ya yi ta yi amfani da zarafin da take da shi. Zurfafa gyare-gyaren da kasar Sin ke yi a gida a dukkan fannoni, ba kawai zai dace da yanayin da ake ciki ba, har ma zai kasance wani bangare ne na nauyin da aka dora wa kasar Sin. Tabbas ne zurfafa yin gyare-gyare da kasar Sin ke yi a dukkan fannoni zai habaka tsarin gurguzu mai halin musamman na kasar Sin, kuma zai samar wa kasar ta wani karfin cimma burinta ba tare da kasala ba.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China