Dangane da lamarin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a yau Alhamis cewa, kasar Sin ba ta yarda da cinikin hauren giwa ba bisa doka ba ko kadan, kuma kasar za ta ci gaba da hada kai da gamayyar kasa da kasa don ganin an hana kashe giwaye da kuma cinikin haurensu ba bisa doka ba, kana ta yi kira ga kasashen duniya da su hada kai wajen ganin an kare giwaye. (Maryam)